(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Yanzu-yanzu: Sheikh Abduljabbar ya karɓi gayyatar yin muƙabala da wasu malaman Kano

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano ta aike da goron gayyatar zama mukabala tsakankin Sheikh Abduljabbar da wasu malamai a jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar Kwamishinan addinai na jihar Kano, Dr Baba Impossible ne ya wakilci gwamnatin jihar wajen kai wa malamin goron gayyatar.

An dai sanya ranar Lahadi, 7 ga watan Maris a matsayin ranar yin zaman muhawarar tsakanin malaman jihar da Sheikh Abduljabbar, malamin da ake zargi da yin kalamai wadanda ba sa yi wa wasu musulmi dadi.

Takadar gayyatar da DABO FM ta ganewa idanunta mai dauke da sa hannun Sheikh Abduljabbar da wakilin gwamnati, ta tabbatar da karbar tahin zaman da malamin ya yi wanda za a gudanar a mako mai zuwa.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog