Copyrighted.com Registered & Protected

Zaben2019: An kama kuri’a a gidan gwamnan Kogi, Yahaya Bello?

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC tayi tsokaci bisa labarin data samu na kama kuri’a a gidan gwamnatin jihar Kogi, kuri’un da rahotan ya bayyana an daddangwalawa jami’iyyar APC a takardar zaben sanatan kogi ta tsakiya.

Rahotanni sunce ‘yayan jami’iyyar APC aka gani da kuri’un a cikin gidan gwamnati.
Da take jawabi, hukumar ta INEC tace wannan labari ba gaskiya bane.

“Mun samu rahoton wasu daga cikin kayan aikinmu suna wajen ‘yan siyasa a jihar Kogi.”

Hukumar tace babu wani kayanta daya shiga hannun dan siyasa ko wani jami’in gwamnati, hasalima kayan a kowacce jiha, suna babban bankin kasa na Central Bank.

“Wannan labarin ba gaskiya bane, domin kuwa duk kayan aikinmu suna babban bankin Central Bank of Nigeria.”

Hukumar ta ja hankali mutane cewa, kuri’a mai stamfi tare da sa hannun jami’in zabe ita kadai ce ingantacciya.

%d bloggers like this: