Siyasa

Zaben2019: Idan Ubangiji ne zai kirga kuri’u babu yadda Buhari zai iya cin zabe – Buba Galadima

Shugaban tafiyar R-APC, jigo a  yakin neman zaben Atiku Abubakar, tsohon na hannun damar shugaban kasa Muhammadu Buhari yace babu yadda za’ayi shugaba Buhari ya samu nasara.

Buba Galadima yayi wannan furucine a wata hira da yayi da sashin Hausa na VOA.

Danna akan tallafa domin taimakamana.

 

Saidai furucine na Alhaji Buba Galadima ya jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, furucine da akeyiwa kallo da yiwa Allah izgili, wanda a fuska ta fannin addinin musulunci bai dace ace mutum irin Buba yayi kalaman ba.

A siyasance wasu na ganin kalaman sunyi dai dai, kuma suna ganin za’a iya yin fashin baki akan furucin da ma’ana kamar haka:

“Indai zaben Allah da annabi za’ayi, babu yadda Buhari zai yi nasara.”

“Indai zabe za’ayi na gaskiya, Buhari bazai samu nasara ba.”

A wani faifan bidiyo da Alhaji Buba ya wallafa a shafinshi na twitter, yace mutane sun juna kalamanshine da wata manufa, amma shi abinda yake nufi ba haka ake fassarawa ba.

“cewa nayi a hira ta da VOA Hausa idan Ubangiji ne zai kirga kuri’u babu yadda Buhari zai iya cin zabe, amma wasu mutane sun je sun sauya abinda na fada saboda tsabar rashin son gaskiya.”

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben2019: Najeriya zatayi asarar biliyan 140, dalilin dage zabe

Dabo Online

Zaben Gwamna: Mal Shekarau yasha kayi a akwatin kofar gidanshi

Kano: Zaben gwamnan jihar Kano yana da gibi, za’a tafi zagaye na biyu

Dangalan Muhammad Aliyu

Zaɓaɓɓen ɗan majalissar jihar Adamawa ya rasu

Dangalan Muhammad Aliyu

Bana bukatar sasantawa tsakani na da Buhari – Buba Galadima

Dabo Online

Zaben2019: Duk bakin cikin su sai na siyar da NNPC – Atiku Abubakar

Dabo Online
UA-131299779-2