(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Za mu karbi sakamakon zabe, fatanmu a zauna lafiya – Kwankwaso

Karatun minti 1

Sanatan Kano ta tsakiya, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso yayi kira ga magoya bayanshi dasu zama masu hakuri tare da tabbatar da zaman lafiya bayan an fitar da sakamakon zabe.

“Ina Godiya ga Allah subhanahu wata ala daya Bamu dama mukayi zabe lafiya muka gama lafiya. Dukda akwai abubuwa da suka faru na rashin jin dadi, amma ina fatan mutane zasu kwantar da hankalin su domin zamu dauki matakai a guraren daya kamata.

Inason injawo hankalin mu da cewa zaman lafiya shi yafi komai muhimmanci, kada muce zamu dauki doka a hannu a wannan lokaci.

Muna fata mutane zasu cigaba da abubuwan daya kamata suyi na shirye shiryen zaben  Gwamna da yan majalisun jiha wanda muke sa rai shima lokaci kadan za’a gudanar dashi a wannan jiha dama Kasa gabaki daya.

A zaben shugaban kasa muna ganin sakamako yanata fitowa dafatan idan aka fitar da sakamako kowa zai karbeshi ta hanyar daya dace.
Muna fata abokan hamayyar mu suma zasu tsawatar wa da magoya bayan su domin asamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan jiha.

Muna addu’a Allah yaci gaba da bamu zaman lafiya a jihar Kano da Kasa baki daya, kuma yabamu nasara na zabubbuka da zasu taso a wannan jiha dama kasa gabaki daya.  Jama’a Nagode.” – Engr Rabi’u Musa Kwankwaso

Karin Labarai

Sabbi daga Blog