(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

#NigeriaDecides2019: Alamu sun nuna kifewar Kwankwaso, Saraki da Dino Melaye

dakikun karantawa

A cigaba da tattara bayanan kuri’un da mutanen Najeriya suka kada, dukkan alamu sun nuna faduwar Kwankwaso tare da ‘dan takarar daya tsayar karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Hon Aliyu Sani Madakin Gini. Tazarar kuri’un da suke tsakininshi da ‘dan takarar jami’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano Mal. Ibrahim Shekaru tanada matukar tsayi.

Ga jerin wasu daga cikin kana nan hukumomin cikin birnin Kano:

Madobi: (Karamar Hukumar Sanata Kwankwaso) 

President:   APC: 26,110               PDP: 13,113

Senate:        APC: 22,731               PDP: 15,524

Rep:             APC: 22,100               PDP: 15,925

 

Gwale:

Senate:              APC: 40,352                  PDP: 21,117

President:        APC: 50,834                  PDP: 12,2783.

 

Shima daga bangaren jihar Kwara, shugaban majalissar dattijai, Dr Abubakar Bukoula Saraki, alamu sun nuna faduwar sanata, inda alkaluma suka nuna abokin hamayyarshi na jami’iyyar APC ya bashi tazarar kuri’u da suka kai sama da 50,000.

Daga jihar Kogi, nan ma bata sauya zani ba, shima Sanata Dino Melaye na fuskantar babban kalubale. Saidai sanatan ya fito ya karyata rahotannin da ake yadawa, inda ya kirashi da shirin gwamna Yahaya Bello nayin magudin zabe kamar yadda zaku gani bidiyon dake kasan wannan rahotan.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog