Zulum ya nemi Najeriya ta gayyato sojojin ƙasar Chadi

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum ya nemi gwamnatin Tarayya ta gayyato sojojin ƙasar Chadi domin haɗa ƙarfi da ƙarfe da sojojin ƙasar nan in dai har ana son kawo ƙasar Boko Haram.

Rahoton Dabo FM ya bayyana Zulum ya yi kiran a ne Maiduguri lokacin da shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, John Kayode Fayemi yaje yin jajen harin da aka kaiwa gwamnan a garin Baga.

Ziyarar ta haɗa da shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP kuma gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya, Solomon Dalung tare da Senator Abubakar Atiku Bagudu wanda suka bada gudun mawar naira miliyan 100.

Zulum ya bayyana cewa “A kowace ƙasa babu sojojin da suke samu nasara idan ana yaƙi ba tare da haɗin gwiwa ba, ya kamata gwamnati ta gayyaci sojojin ƙasar Chadi domin haɗa ƙarfi da ƙarfe.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog