‘Yancin kan Najeriya: Gwamma jiya da yau -Marafan Yamman Zazzau

dakikun karantawa

Duk da wasu batutuwa na cigaba da jawabin shugaban kasa Buhari ya mayar da hankali lokacin da ya gabatar na cikan kasar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kanta, wasu yan Najeriya na cigaba da bayyana cewa a halin da Najeriya ke ciki yanzu za’a iya cewa gunma jiya da yau.

Marafan Yamman Zazzau Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu shi ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai game da cikar Najeriya shekaru 60 da samun yancin kanta daga turawar mulkin mallaka na kasar Burtaniya.

Ya ce, abubuwa da dama da suka shafi cigaban kasa da suka hada da tsaro da tattalin arziki da zamantakewa babu wani abu na a zo a gani da wannan gwamanti ta kawo domin saukakawa yan Najeriya ta wannan fuska, tunda har yanzu talakawa na cikin ukuban yunwa da fatara da kuma talauci.

Ya kara da cewa, ko a siyasance yanayin da ake ciki babu wani canji tunda kusan jagororin da suke rike da madafun iko a yau sun kasance tare da Jama’iyyar PDP a lokutan baya, amma yau Jama’iyyar ta PDP ce abun zagi a wurin su saboda ana damawa da su a gwamnati.

Bngaren Noma kuwa, ya ce shi a ganin sa babu wani tasiri ko cigaba da aka samu a bangren banda bakar wahala da mutane ke sha saboda naiman bashin aikin Gona. Kuma an kasa wadata yan kasa da kayayyakin aikin da suka dace domin habbaka bangaren.

Marafan Yamman Zazzau ya ce, halin da yan kasa ke ciki yanzu ba’a fatan cigaba da dawwama a kai, domin mutane kalilan ne ke cin gajiyar gwamantin da ake kurarin kuma ana yi ne domin al’umma.

Ya dora koma bayan da aka samu a kasar nan ga gwamnati mai ci da kuma ‘yan siyasa marasa kishi da son cigaban kasa.

Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu, ya tunatar da jagorori su rika tunawa da nauyin al’umma da ya rataya a kan su kuma su sani Allah mai tambayar su ne kan abun da suke aikatawa ranar gobe Alkiyama..

Da ya juya ga halin da ake ciki a Jihar Kaduna kuwa na rashin nada sabon Sarkin Zazzau, uban al’umman, ya nuna takaici kan yadda gwamna Nasiru El-rufai ke jinkiri wurin sanar da wanda zai gaji Marigayi Mai Martaba Sarki Zazzau Alhaji Shehu Idris da Allah ya yi ma rasuwa kwanakin baya.

Ya tunasar da gwamnan game da maganar da ya yi lokacin da yake jawabin bayan kammala addu’an cika kwanaki Uku da rasuwar Sarkin, Da ya yi kira ga Wazirin Zazzau da sauran masu zaben Sarki su zakulo haziki da zai daura kan kokarin da Marigayi ya yi na aza masarautar Zazzau ga turbar da ta dace.
Kuma ya ce jinkirin ba zai haifar da d’a mai ido ba sai dai kawo koma baya ga masarautar da Jihar Kaduna.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog