Buhari zai siyar da NNPC

Karatun minti 1

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa Majalissar tarayyar wasu kudure-kudurai da za kawo karshen mallakar da gwamnati take yi wa Hukumar NNPC.

Tuni dai Shugaban Majalissar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya sanar da zuwan kudirin, ya kuma ce majalissar za ta duba.

Kudurin ya kuma nemi majalissa ta bawa gwamnati damar kashe hukumar PPPRA da take kula da farashin mai a Najeriya.

Kudurin ya ce za hukumar NNPC za ta dena amsa kiranta a matsayin hukuma, za ta koma NNPC Limited.

“A bisa sashi na 53 na kudurin, bayan kammala tattara dukkanin kadarorin NNPC, Minista (Na mai) zai  yi mata rijista da sunan Nigerian National  Petroleum Company Limited.”

“Minista ( Na Mai) zai kasance a wajen yin rijistar, za kuma su tattauna da Minista (Ta Kudi) domin a fitar da yadda za a siyar da hannun jari ga ‘yan kasuwa.”

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog