Kotun daukaka kara ta baiwa ‘Abba Gida-Gida’ damar kara shedu a cigaba da shari’arshi da Ganduje

by Dabo Online
0 comments

Kotun daukaka kara dake da zama a jihar Kaduna ta umarci kotun sauraren korafe korafen zaben gwamnan jihar Kano da ta bawa PDP damar yin sauyi tare da karin shedu da zata gabatar a gaban kotun.

Hakan na zuwa ne bayan da kotun sauraren korafe korafen zaben Kano tayi watsi da bukatar PDP na karin sunayen shaidu 8 akan zaben gwamnan Kano da take kalubalanta.

Jami’iyyar tace wadannan shedun guda 8 sune daga cikin manyan shaidun da take som gabatarwa.

Hakan yasa jami’iyyar PDP da dan takararta, Abba Kabir Yusuf suka daukaka kara a ranar 16 ga watan Yulin 2019.

Da suke jawabi ta hannun lauyoyinsu, hukumar INEC da APC sun bayyana cewa zasu daukaka kara zuwa kotun koli.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00