Kotun dake shari’ar shugaban kungiyar IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta yanke ranar 5 ga watan Agusta don yanke hukunci akan neman beli da shugaban ya gabatar.
A ranar 18 ga watan Yuli ne dai lauyan Al-Zakzaky, Femi Falana SAN, ya aike da bukatar bada belin shugaban na IMN.
Al-Zakzaky yana neman samun izinin tsallakawa kasar Indiya domin duba lafiyarshi bisa yanayin rashin lafiya ta tsanana da yake fama dashi a inda ake tsare shi, a cewar lauyan Al-Zakzaky.
DABO FM ta binciko cewa Al-Zakzaky bai samu halartar zaman kotun ba, sai dai lauya mai kare shi, Mista Falana, yace rashin zuwan nashi yana da nasaba da tsananin rashin lafiyar tashi.
Femi Falana, ya kara da cewa; A yanayin lafiyar Al Zakzaky, duba lafiyarshi a kasar waje ne abinda yafi dacewa kuma shine dalilin da yasa suke neman izinin kotun da ta bada belinshi.
Sai dai a nashi bangaren, lauyan masu kara, Debris Bayero, ya soki lamirin bada belin Zakzaky.
Mista Debris yace babu lallai sai an fitar da shugaban na IMN, Sheikh Zakzaky zuwa kasar waje, domin za’a iya duba lafiyarshi tare da bashi kulawa a gida Najeriya.
Bayan jin ta bakin kowa, mai shari’a Darius Khobo, ya dage zaman zuwa ranar 5 ga watan Agusta domin yanke hukunci akan bada belin.
