0
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta ragargaza Man UTD da ci 4 babu ko 1.
Kungiyar data karbi bakuncin Man UTD a filin wasa na Camp Nou ta lallasa Man U ta hannun Lionel Messi tare da Countinho.
Messi ne ya fara zura kwallo a ragar Man UTD a minti na 16, inda ya kara zurawa a minti na 20 kafin dan wasa Philippe Coutinho ya zura ta 3 a minti 61.
Barcelona ta hada jimillar kwallaye 4 a ragar Man UtD, a wasannin da aka buga a Old Trafford da Camp Nou.
Barcelona ta samu damar tafiya zagen daf dana karshe, inda zata kece raini da kungiyar da tayi nasara gobe tsakanin Liverpool da FC Porto.
