Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta lallasa abokiyar karawarya Juventus da ci 3 da 2.
Kungiyar ta Ajax ta murza leda yadda ya kamata inda ta bawa Juventus wuya tin a wasan farko da aka buga wanda aka tashi chanjaras a gidan Ajax.
Dan wasa Cristiano Ronaldo ne ya fara jefa kwallo a ragar Ajax cikin minti na 28, inda daga bisani kuma dan wasa Donny Van Beek ya farkewa Ajax a minti na 34.
A minti 67 ne dai dan wasa Matthijis de Ligt ya kara zura kwallo a ragar Juventus.
Ajax ta samu nasarar zuwa zagayen daf dana karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai inda zata kara tsakanin wanda yayi nasara gobe, Man City ko Tottenham.
Kungiyar Ajax dai itace tayi waje da kungiyar Real Madrid tin a zagaye na 16.