Oshiomhole ya bayyana haka ne a taron ganawa da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi da zababbun ‘yan majalisar Tarayya na jam’iyyar APC a fadar gwamnati ranar Talata.

Adams ya bayyana haka ne a wani taron zababbun ‘yan majalissun APC da aka gudanar a fadar shugaba Muhammadu Buhari a jiya Talata.

“Mun tafka kuskure a shekarar 2015 wajen zabe shuwagabanni, amma yanzu bazamu yadda muyi kuskure ba. ‘Yan jami’iyyar mune  kawai zasu rike manyan mukamai a majalisa.

Babu dan jami’iyyar adawa ko daya da zai rike wata babbar kujera a majalissar.” – Adams Oshiomole

Jaridar Premium Times ta rawaici wasu daga cikin jawaban Adams Oshiomole kamar haka;

” Da ‘yan Najeriya na son su da sun zabe su wato PDP din. Kuma ida ba a manta ba a zamanin da suka sheke ayar su ay sune suke raba wa kansu kujerun shugbancin na kwamitin majalisa.

” Da dadaddun ‘yan majalisa da sabbi duk za a nada su shugabannin kwamitoci. Kowa zai samu abu a majalisar.