(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Abduljabbar cikakken maƙaryaci ne – Ganduje

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya cika babban maƙaryaci.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata gajeriyar tattaunawarsa da sashin Hausa na BBC a yayin da yake martani kan kalaman Sheikh Abduljabbar bayan gwamnatin ta dakatar da shi.

DABO FM ta tattara cewar gwamnatin jihar dai ta dakatar da malamin sakamakon kalaman tunzura jama’a da gwamnatin ta ce yana yi.

Ganduje ya ce; “Maganganunsa akwai da yawa a ciki. Kamar misalin da ya bayar ya ce kwamishinan ilimi ya yi hira a rediyo ya ce shi aka zalunta, to karya yake yi. Kwamishinan ilimi bai ce an zalunce shi ba.

Gwamnan ya ce kwamishinan ya bada tarihin yadda aka kwace filin a wata gwamnatin baya. Ya ce filin yana hannun gwamnati kuma ta yi makarantar matan aure a wajen.

Kazalika gwamnan ya ƙalubalanci malamin da ya kawo sautin muryar da kwamishinan ya ce an yi masa zalunci.

A gefe guda kuma al’ummar musulmi suna zarginsa da aibata sahabban annabi Muhammad SAW.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog