Mahaifin fitaccen mawaƙin Hausa na zamani, Ali Isa Jita ya rasu a jiya Juma’a.
Mawakin ne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yau Asabar.
Ya ce; “Ina baƙin cikin sanar da mutuwar mahaifina, Alhaji Isa Jibril Kibiya.”
DABO FM ta tattara cewa za a yi jana’izar marigayin yau Asabar da misalin ƙarfe 9 na safe a gidansa da ke unguwar Shagari Quaters da ke cikin birnin jihar Kano.