Boko Haram sun sake afka wa tawagar Zulum, sun kashe ‘Yan Sanda da Sojoji

Karatun minti 1

Mayakan kungiyar Boko Haram sun sake afka wa tawagar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a karo na biyu.

Rahotannin sun ce mayakan sun afka wa tawagar gwamnan a kusa da garin Baga dake daura da gabar Tafkin Chadi   a ranar Juma’a cikin wani shiri da Gwamnatin jihar take yi na mayar da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu.

Mayakan kungiyar sun bude wa tawagar gwamnan wuta da Bindiga Mai Sarrafa kanta da Bindigar Roka a dai dai lokacin da tawagar take wucewa a kusa da wani Kauye kusa da Shedikwatar jami’an hadaka dake yaki da kungiyar ‘yan ta’addar.

Wasu majiyoyi da suka yi nemi a sakaya sunansu sun bayyanawa kamfanin Labarai na AFP cewa gwamnan ba ya cikin tawagar,  ya hau Jirgi Mai saukar Ungulu don zuwa garin na Baga.

Wasu majiyoyi sun tabbatarwa kafar cewa mayakan Boko Haram sun kashe a kalla Jami’an tsaro 15 da suka hada Yan sanda, Sojoji da CJTF.

Wannan ne karo na biyu da mayakan Boko Haram suka afka wa tawagar Gwamnan, bayan da suka afka masa a watan Yuli.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog