(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Biyan Albashi: Bance kar a biya ma’aikata N30,000 ba – Kwankwaso

dakikun karantawa
Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso

A daren jiya Alhamis, wasu labarai a  kafafen yada labaran yanar gizo gizo sukayi ta yada zancen cewa Kwankwaso ya umarci dan takarar gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf da kada ya biya N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

[irp posts=”4518″ name=”Arewa nada bukatar Jagororin irin Kwankwaso – Sheikh Ibrahim Khalil”]

Sai dai a wani sako da mataimakiyar Kwankwaso a fannin labarai, Haj Binta Spikin tace wannan magana ce da bata da tushe, kuma duk wanda yasan Engr Kwankwaso yasan bazaiyi wadannan kalamai ba.

“Mun samu labarin wasu jaridu da kafafen yada labarai irinsu Daily Trust, Sahara Reporters da sauransu, suna yada maganar cewa Kwankwaso ya umarci Abba kada ya biya 30,000 idan an zabe shi. Muna kira ga mutane da kada su yadda da wannan labari domin bashida tushe kuma duk wanda yasan abinda Kwankwaso yayi na jin dadin ma’aikatan Kano yasan bazai fadi haka ba.”

[irp posts=”4293″ name=”Kwankwaso bashida takardun kammala Firamare – Ganduje”]

“Gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin wannan maganar domin a batawa Kwankwaso da ‘dan takararmu suna.”

“Abinda yake gabanmu yanzu shine shiri domin ganin an gudanar da karashen zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da rashin adalci ba.”

“Daga nan zuwa 23 ga watan Maris, mutane zasu rika ganin irin wadannan karairayin da gwamnatin Kano ta dauki nauyin su a Jaridar Daily Trust, Sahara Reporters, Legit Hausa NG da dai sauran kafafin sadarwa.”

A karshe tayi kira da mutane da suyi watsi da wadannan labarai domin ba gaskiya bane.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog