Kano: In bidiyon da aka ganmu gaskiya ne a ina aka ga mun yaga takardar zabe? – Murtala Garo

dakikun karantawa

Kwamishan kananan hukumomi na jihar Kano, Hon Murtala Sule Garo yace su ba barayin takardar tattara sakamakon zabe bane.

A wani taro da kwamishinan yayi da manema labarai ya bayyana cewa shi bai yaga takardar zabe ba, kamar yadda ake zarginsu da aikatawa, har ma yace idar har da gaske zargin da akayi musu na gaskiya ne, to a fito da hoto ko bidiyon da aka gansu a lokacin da suke yaga takardun.

[irp posts=”4497″ name=”ZabenKano: ‘Yan sanda sun cafke Kwamishina, bayan yunkurin keta takardar tattara sakamako”]

Ya kara da cewa, wakilan jami’iyyar PDP ne suka yaga takardar sakamakon zaben tin kafin zuwansu wajen tattara sakamakon.

“Biyu daga cikin ma’aikatan hukumar INEC sun bada tabbacin cewa Alhaji Faruk Lawal tare da Alhaji Sule Garo ne suka jagoranci yaga takardar.” – Murtala Garo

Kwamishan ya ce wannan sharri ne kawai irin na siyasa aka shirya domin a bata masa suna tare da mataimakin gwamnan, Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

[irp posts=”4508″ name=”ZabenKano: ‘Yan sanda sun cafke mataimakin Ganduje, bayan yunkurin sace takardar tattara sakamako”]

“Na samu kira daga wani wakilin jami’iyyarmu ta APC akan abinda ‘yan PDP suka aikata. Na kira mataimakin gwamna domin sanar dashi halin da ake ciki. Nan take ni da shi tare da shugaban karamar hukumar Nassarawa muka kama hanya domin zuwa wajen mu ganewa idanunmu. Wannan shine dalilin daya kaimu wannan waje, amma zuwanmu keda wuya sai wasu bata gari suka kala mana sharrin cewa mune muka yaga takardar, wannan shine yayi sandiyyar kame mu da ‘yan sanda sukayi. Idan har da gaske mun yaga takardar to a ina INEC ta samu waccce ta sanar da sakamakon ta.”

[irp posts=”4508″ name=”ZabenKano: ‘Yan sanda sun cafke mataimakin Ganduje, bayan yunkurin sace takardar tattara sakamako”]

“Kowa yaga yadda mutane suka rika binmu suna zaginmu har zuwa ofishin yan sanda. In takaice ma har cikin ofishin ‘yan sandan  suka bimu sunata fadar magan-ganu marasa dadi kuma ‘yan sandan basu taka musu birki ba.”

Daga karshe kwamishinn ya kalubalanci kwamishan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili akan nuna goyon bayanshi ga bangaren jami’iyyar hamayya ta PDP.

A daren ranar Lahadi ne dai yan sandan jihar Kano suka kame mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Yusuf Gawuna tare da kwamishan Kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule Garo hadi da shugaban karmar hukumar Nassarawa bisa zarginsu da yaga takardar tattara sakamakon zabe.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog