Buhari zai kawo ƙarshen tsadar kaji domin sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya

Karatun minti 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar kawo karshen hauhawar farashin kaji a fadin Najeriya baki daya.

Rahoton Dabo FM ya bayyana shugaba Buhari ya bada umarnin a fitar da masara tan dubu 30 daga ma’ajiyar gwamnatin tarayya domin tallafawa masu kiwon kaji saboda kawo karshen tsadar abincin kaji.

Wannan na zuwa ne cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a shafukan sa na sada zumunta a ranar Alhamis da misalin karfe 10:19 na safe.

Buhari ya fara da cewa “Domin saukaka tsadar kayan abincin kiwon kaji, na bayar da umarnin a fitar da tan 30,000 na masara ga masu kiwon kaji.”

Wannan na zuwa ne bayan da al’ummar Najeriya ke kukan tsadar kayan abinci, karin kudin man fetir da na wutar lantarki da gwamnatin Buhari tayi a cikin satin nan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog