An sake bude kasuwar Sabon garin Zariya

Karatun minti 1

Tun bayan rufe kasuwanni da gwamantin Jihar Kaduna ta yi saboda barkewar annobar Covid-19, daga karshe dai gwamantin ta sanar da bude kasuwan Sabon garin Zariya da wasu kasuwanni da ake gudanar da harkokin yau da kullum a yankin.

Dabo FM ta tattaro cewar bukin bude kasuwar ya biyo-bayan cika sharuddan da Kungiyar ‘yan kasuwan ta yi ne, na cika ka’idojin da gwamanti ta sanya domin kariya daga cutar Covid-19.

Tun a safiyar jiya litini ne dai ‘yan kasuwan ke dakon bude masu kasuwannin, amma daga karshe sai a Talatar nan 1 ga watan Satumba aka sake bude kasuwan.

Yanzu dai ana sa ran za’a cigaba da gudanar da harkokin kasuwan kamar yadda aka saba a baya, amma bisa cika sharuddan kariya daga cutar sarkewar numfashi ta Covid-19.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog