Kano: KAROTA sun fara kamen masu hawa babur ba tare da takardar izini ba

Karatun minti 1

Hukumar kula da cunkoson ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA ta fara kamen masu hawa baburan da ba’a basu shaidar izinin tuƙi ba.

Dabo FM ta rawaito ɗaya daga wanda aka kama mai suna Khatimu Kulkul wanda ke zaune a unguwar Yalwa, karamar hukumar Dala shine ya tabbatar da faruwar hakan.

Khatumu ya kuma zargi jami’an hukumar da kama shi sakamakon ya sanya jar hula, wadda ita ce alamar dake nuni da shi ɗan jamiyyar adawa ne.

Bayan kamun kuma ya bayyana an bashi takardar shaidar kamun da take nuni da an kama shine dalilin bashi da shaidar izini ta tuƙi.

Shima wani mai babur ya bayyana mana cewa hakan ta faru dashi a ranar 13 ga Oktobar 2020.

Bincike ya tabbatar mana babu wata hukuma da take bada shaidar izinin tuƙin babur a fadin jihar Kano baki ɗaya.

Cikin saɗara ta 16,17 da 18 na kundin tsarin hukumar babu inda aka ambaci a nemi shaidar tuƙu ta babur. Kamar yadda The Mail News Online ta fitar.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog