CGE ta yi bikin Ranar Mata ta Duniya

dakikun karantawa

A cigaba da bukin ranar ‘ya’ya mata ta duniya da aka gudanar a lahadin da ta gabata, Cibiyar bunkasa Ilimin mata ta center for girls education wato CGE a turance kuma a takaice, ta shirya taro domin murnanr wannan rana da fadakar da su kan matsalolin da ke damun mata na yau da gobe.

Sa’ilin taron, an gudanar da mabanbanta jawabai daga iyayen al’umma, Farfesa Aisha Indo Mamman, kwararriyar likita ce da ke aiki a Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Shika Zaria, ta ce mata na fuskantar koma baya saboda matsalolin cin zarafi da tilasta masu aikin karfi da kuma rashin samun ingantaccen Ilimi.

A cewar ta, akwai cututtuka da mata ke fuskanta a yau da silar su shi ne rashin samun cimaka mai ingaci da zubar jini da kuma wasu cututtuka da suke kawo cikas musamman lokacin haihuwa, wanda wani lokacin akan rasa yara ko mata wurin haihuwa.

Ta kara da cewa, yanda taga Cibiyar ta bunkasa Ilimin mata ta CGE na taba zuciyar mata da wayar masu da kai game da abubuwan da suka shafi Ilimi da sana’o’i ya bata sha’awa kwarai da gaske domin ta haka ne za’a kai ga matakin da ake bukata na bunkasa rayuwar mata a yau.

Ita ma shugaban makarantar Rochas da ke Zariya Hajiya Rabi’atu Ibrahim ta ce dole iyaye sai sun cigaba da sanya ido kan rayuwar yaran su saboda yanayin da ake ciki na tursasawa da tsana da ake nunawa mata wanda kuma silar wannan shi ne rashin Ilimi. Kuma ta nuna damuwar kan wata matsala da ta taso da ake zargin wani mahaifi da lalata da ‘yar sa a wani yanki, kuma ta ce dole ne maza su kawar da hankulan su ga mata domin samun saukin abubuwan da ke faruwa.

Hajiya Rabi’atu Ibrahim ta yaba ma gwamantin Jihar Kaduna saboda matakan da take dauka kan irin wadannan matsaloli kuma ta bukaci karin wayar da kai da sanya hannu daga kowwani bangare. Su kuma iyaye su guji tura yara talla na babu gaira babu dalili.

Da take nata jawabin Daraktan Cibiyar Ilimin ‘ya’ya mata ta CGE Hajiya Habiba Muhammad Ta yaba ma iyayen al’umma da shuwagabannin addini ne bisa hadin da suke samu daga fangaren su domin kaiwa ga manufar da ake bukata na wayar da kan mata da basu nagartaccen ilimin da za su dogara da kan su.

Shugaban ta kuma bukaci yaran da ke samun horo daga Cibiyar su cigaba da yada Ilimin da suke amfana da shi duk inda suka tsinci kan su domin taimakon juna da kuma yara masu tasowa.

Sa’ilin taron an baje kolin kayayyakin sana’o’i da Cibiyar ta horas da wasu daga cikin daliban da ke karatu karkashin ta da kuma gudanar da wasannin fadakarwa da wayar da kai kan fannoni daban-daban.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog