CNG ta shawarci sabon Sarkin Zazzau ya mai da hankali bangaren inganta tsaro

dakikun karantawa

Hadakar kungiyoyin matasa ta Arewa wato Collation for Northern Groups a turance, ta kai ziyarar taya murna ga sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a fadar sa da ke cikin birnin Zariya.
Ziyarar da ta gudana bisa jagorancin wakilai daga matakin kasa da jiha da kuma karamar hukuma ta kungiyar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa ziyarar taya murnar da kuma mubayi’ar, mai magana da yawun kungiyar ta CNG ta kasa Abdul’azizi Suleiman, ya ce lokacin rasuwar Marigayi Mai Martaba Sarki Alhaji Shehu Idris sun zo ziyarar ta’aziyya da nuna alhini na rashin Uba ga Kasa baki daya, kuma suka yi addu’an Allah rahimin Sarki ya gafarta masa ya sa yana kyakkyawan matsayi.
Shiyasa kuma da aka sanar da magajin shi, suka sake zuwa domin taya murna da jaddada goyon bayan da suke baiwa Sarakuna iyayen kasa ga sabon Sarkin domin kaiwa ga manufofin da ake bukata na ciyar da yankin Arewacin Najeriya gaba.

Kuma ya yi kira da babbar murya ga mai Martaba Sarki ya fara da sanya ido kan abubuwan da suke faruwa a masarautar sa na rashin tsaro da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan karamar hukumar Giwa.
Wanda ya ce ko daren Asabar mahara sun kai mummunan hari a yankin Kidan-dan kuma suka kashe mutane da dama.

Ya yi kiran daukar karin matakai masu tsauri daga jami’an tsaro saboda yadda hare-haren ke sabbaba asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.

Abdul’azizi Suleiman, ya sake tabbatar da aniyar Kungiyar su ta baiwa sabon Sarki da bangaren hukumomin tsaro goyon baya domin kaiwa ga gaci.

Kuma ya ce, suna nan kan manufar su ta cigaba da kare daraja da mutuncin Arewa a koda yaushe.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog