/

Kirsimeti: Biki ne na tuna wa da sakon da Almasihu ya bari -Yohana Sarki

dakikun karantawa

A ranar 25 ga watan Disamba ce, miliyoyin mabiya addinin kirista suka gudanar da bikin ranar harhuwar Annabi Isa, na shekaru 2020.

A kullum shuwagabanni suna mika sakon zaman lafiya ga mabiyansu, inda suke kira da su zauna lafiya tare da bin karantar Annabi Isa domin a samu ci gaban kasa.

A wannan shekarar ma shugaban kungiyar kiristoci ta Kasa reshen karamar hukumar Kudan ta Jihar Kaduna Rabaran Yohana Sarki ya mika sakon ranar kirsimiti ga mabiya addinin kirista baki daya.

A wannan sakon kirsimeti ga ‘yan kasa, Yohana Sarki, ya bukaci dukkan ‘yan Nijeriya da su so junansu tare da hada kai ga dukkan kabilun kasar nan, ta yadda za’a samu dangantakar juna tare da hadin kai a tsakanin ‘yan kasa gaba daya. Haka kuma, ya shawarci ‘yan Nijeriya su yi amfani da wannan bikin kirsimeti wajen yin addu’o’i ga matsalolin da ke damun wannan kasa, kamar su ta’addanci da fashi da makami da masu garkuwa da mutane da kuma matsalar tattalin arziki, domin ci gaban kasa.

Ya kara da cewa, kirsimeti lokaci ne da daukacin kiristoci ke tura sakon fatan Alheri ga juna.

Haka kuma, lokaci ne na yin addu’o’i ga ‘yan’uwa da abokan arziki da kuma addu’o’i fita daga cikin matsin tattalin arziki. A bangaren yara kuwa, wannan lokaci ne na saka sababbin kaya da da shagulgula, wannan lokaci ne na siyan kayayyakin abinci da nama da kayayyakin marmari. Haka kuma, lokaci ne na bayar ga kyaututtuka ga masoya.

Rabaran Yohana Sarki ya kara da cewa biki ne na tuna wa sakon da Almasihu ya bari a wannan lokaci.

Daga nan sai Yohana Sarki ya yabawa shugaban karamar hukumar Kudan Alhaji Shu’aibu Bawa Jaja saboda irin taimakon da hadin kan da yake basu koda yaushe kuma ya yi fatan sauran Shuwagabanni su yi koyi da hali irin nashi domin samun al’umma ta gari.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog