(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Duban Lafiyar Sheikh: Kasar Iran ta yabawa shugaba Buhari kan El-Zakzaky

Karatun minti 1

Gwamnatin kasar Iran ta yabawa shugaba Muhammadu Buhari bisa barin manyan likitoci daga kasar waje domin duba lafiyar Sheikh Zakzaky tare da matarshi.

Kasar ta fitar da sakon yabon ne a yau Asabar, daga hannun mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin kasashen waje ta kasar Iran, Seyed Abbas Mousavi.

Kasar ta jinjinawa shugaba Buhari tare da fatan hakan zai bude kofar tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da ‘yayan kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi ta Najeriya wato Shi’a.

Yace yana gani hakan zai kawo karshen tsare Malamin da gwamnatin Najeriya take yi.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa, Gwamnatin Najeriya ta bar wasu manya likitoci domin duba lafiyar Sheikh Zakzaky tare da matarshi a karon farko tin bayan tsare malamin a shekarar 2015.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog