Binciken Turawa yace Sarauniyar Ingila “Elizabeth” ta hada jini da Annabi Muhammad “SAW”

dakikun karantawa

Tsohon ikirarin da masarautar Biritaniya na cewa Sarauniya Elizabeth tanada asali ko dangantaka da Annabi Muhammadu S.A.W, ya sake bayyana inda aka cigaba da gudanar da bincike akan hakan.

Jaridu a kasar ta Birtaniya irinsu, Daily Express, Daily Mail da Jaridar “Al Ousboue” ta kasar Morocco dama wasu manyan Jaridu a kasar Senegal sun wallafa binciken da masana sanin dangogi suka gudanar tsakanin alakar Annabin Rahama Muhammad ‘SAW’ da sarauniyar Birtaniya, Elizabeth ta Biyu.

“Su waye a dangin Elizabeth ta biyu? Kowa zai yi tunanin asalinta daga daga manya-manyan sarakunan nahiyar Turai yake, babu wanda zaiyi tunanin saka Annabi Muhammad acikin jerin dangin sarauniyar.

Sai dai idan ka bude shafukan yanar gizo da wasu littafai na Birtaniya a kwanakin nan sun tafi akan cewa sarauniyar daya ce daga zuriya Annabi Muhammad “SAW”

Shin ta tabbata cewa lallai Sarauniyar nada alaka da Annabi Muhammad? Sukace ya rage na mai karatu ya yarda da tushen tarihin da zasu fada ko barranta daga haka. 

Kamar yadda Economists Notes suka fada, masarautar ta fara ikirarin kan alakar tin shekarar 1986,  binciken ya samu asaline tin lokacin da Harold B. Brooks-Baker, wani kasaitattcen masanin tarihin dangogi ya fara yi a shekarar.

Brook Baker ya aikewa da Firaministan Birtaniya, Margaret Thatcher, na wancen lokacin cewa ”Mutanen Birtaniya kalilan ne suka san cewa da jinin Annabi Muhammad a jikin Sarauniya.

Brook Baker ya hado dangantakar Annabi Muhammad ‘AS’ da Zaida.

Zaida ta kasance musulma a karni na 11, wacce daga bisani ta koma addinin kiristanci bayan Sarki Alfonsu na 6 ya cinye su da yaki, hakan yasa aka kamata a matsayin garkuwa, inda daga bisani Sarkin ya aure ta. 

“Sai dai sunce basu tabbatar da cewa Zaida tana da alakar jini da Annabi Muhammad ‘AS’ ba.


Zaidar Masarautar Seville ta daular Andalus

Shima a nashi bangaren, Abdelhamid Al-Aouni, wani masanin tarihi, yayi rubutu mai taken “Al-Ousboue” inda ya tabbatar da cewa lallai akwai alaka tsakani. 

Ya tabbatar da Zaida a matsayin wacce ta hado dangantakar. Yayi amfani da Zaida wajen bin salsalarta har zuwa karni na 43 na baya har zuwa Annabi Muhammad ‘SAW’.

Kalli Bidiyon don fuskantar yadda masana tarihin suka bayyana salsalar.
Bidiyon baya nuni ko kasancewa hujjar rahoton da muka rika.
Za’a iya kallon tallar da DABO FM ba tada hannu aciki.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog