Babban Sifetan ‘Yan sandan Sri Lanka ya ajiye aiki bisa mutuwar mutane 320 a harin ta’addanci

Babban Sifetan ‘Yan sandan kasar Sri Lanka, Pujith Jayasundara ya ajiye mukaminshi na zan ragamar rundunar yan sandan ta kasar Sri Lanka a jiya Juma’a data gabata.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kai harin ta’addanci ranar murnar bikin Ester wanda ya hallaka kimanin rayuka 320.

Jaridar The Hindu ta kasar ta rawaito cewa babban Sifetan ya ajiye aikin ne bisa umarnin shugaban kasar Maithripala Sirisena wanda ya aike masa kwana biyu bayan an kai hari a wasu cocinan kasar yayin bikin Ester na addinin Kiristanci.

Shugaban kasar Mr Sirisena yace baban Sifetan ya ajiye aikin ne bisa sakacinshi wanda yakai ga harin da yan tada kayar baya suka kai a Otal 3 da cociya 3 a kasar, wanda hakan yayi sanadiyya rasa rayukan mutane kusan 253.

“Shugaban ‘Yan sanda ya ajiye aikinshi. Ya tura takardar ajiye aikin zuwa babban ofishin kasar. Zan zabi wanda zai maye gurbinshi.” – cewar shuagaba Sirisena

Shima babban sakataren tsaron kasar, Hemasiri Fernando ya rubuta tashi takardar ajjiye aikin ranar alhamis, kwana daya kafin ajiye aikin babban Sifetan ‘yan sandan.

%d bloggers like this: