(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Hannunka Mai Sanda: Aisha Buhari ta kara caccakar shugaba Buhari

dakikun karantawa

Mai dakin shugaba Muhammadu Buhari, Haj Aisha Muhammadu Buhari, yayi wata kakkausar suka ga Mai gidan nata, sukar da majiyoyinmu suka bayyana da hannunka mai sanda.

Majiyoyin DaboFM sun rawaito Aisha Buhari ta wallafa wani faifan bidiyo a shafinta na manhajar Instagram dake magana akan irin maganganu data saba yi na fadawa duniya cewa akwai wasu shafaffu da mai wandanda suke gudanar da sha’anin mulkin Najeriya bayan mai gidan nata shugaba Muhammadu Buhari.

Bidiyon da Julius Malema, tsohon dan takarar shugabancin kasar Afrika ta Kudu, yake aikewa da sakon taya muryarshi ga shugaba Cyril Ramaphosa wanda ya lashe zaben kasar na 2019.

Malema yana cewa; “Muna taya ka murna, kuma muna fatan zaka gudanar da mulkin da babu masu cin hanci da rashawa a ciki.”

“Muna fatan bazaka kar kata da jin shawarar wadansu shafaffu da mai ba, sune mutanen da suka dabai baye shugaban kasa, masu fada maka abinda kakeson sonji. Sakamakon haka sai ka kasa yanke abinda yake dai dai , sai wanda suke so.

“Na lura munada matasa masu basira da sabbin tunani da zasu iya taimaka maka, masu rikon amana da zasu tafiyar da mulkin kasa.

“Akwai masu mukaman da sun aikata abu na ba dai dai ba, an fada musu kuma kowa ya sani, amma sunayiwa kansu kallon abinda sukeyi dai dai ne ko da kuwa kotun shari’a tace abinda suka aikata ba dai dai bane.”

DaboFM ta binciko cewa Uwargidan shugaba Buhari ta saba wallafa bidiyoyin da ake sukar gwamnatin da wadansu mutane suka dabai baye.

Aisha Buhari ta kasance mai sukar lamirin gwamnatin shugaba Buhari ce da abinda ta kira masu guya mijinta nata da shaffafu da mai.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog