Copyrighted.com Registered & Protected

Yunwa, Talauci, Tashin hankali da bala’i kawai ake fama dashi a Najeriya – Sheikh Muhd Nasir

Babban Limamin masallacin Waje, Wazirin Kano Murabus, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad ya bayyana kokenshi kan yacce al’ummar Najeriya suka tsinci kawunansu na gurbataccen jagoranci.

Majiyoyin DaboFM sun tattaro Sheikh Nasir yayi wannan kakkausar magana dai dai lokacin da yake gabatar da Tafsirin Al-Kur’ani mai girma a jihar Kano.

“Ga zalinci ga cuta kullin, wannan ya kwashe arzikin wancan ya kwashe, duk Allah ya tara ya jarrabemu da barayi.”

“Tinda ake a najeriya ba’a taba shiga mummunan hali irin wannan ba, yunwa, takauci, tashin hankali, ba irin musibar da babu ita a najeriya yanzu, saboda mutane sunce allah bai iya ba, sun bashi, sunce wanin allah shine zai musu.”

Masu Alaƙa  'Azumin Sittu Shawwal bashida asali, yin shi Bidi'a ne'

“To gashi, Innalillhi wa’inna Ilaihirraji’un, Allah ya daura mana lalatattun da bamu taba gani ba, tin daga kan Sardauna da Tafawa Balewa, bamu taba ganiin lalcewar shugabanci irin wannan ba, amma dan ha’inci da yaudara da rashin sani da tsoron Allah, wai wadannan mutanen ake bi, anayi musu fadanci ana cewa su mutane ne ne.”

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: