Babu wanda Mata suke So iri na, me zanyi da Aure? – Adamu Zango

Adam A. Zango, Jarumi a masana’antar fina-fina ta Kannywood ya bayyana cewa ‘yan mata sunfi sonshi akan kowa dake masana’antar fim, don haka me zai yi da aure.

Adam Zango ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, inda yake amsa tambayoyi akan auri saki da yake yi.

Hirar Zango akan maganar auren cikin hotuna;

“Saboda ni Adamu Zango, Allah ya ba ni, duk duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda mata ke so iri na. To me zan yi da aure?”

A baya dai, DaboFM, mun rawaito kuma maganar Zango yana cewa ”Mai Auri-Saki ba mazinaci bane.”

%d bloggers like this: