(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Idan shinkafa ta gagare ku, ku ci dabino -Shehu Sani ya rarrashi ‘yan Najeriya

Karatun minti 1
Kwamared Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna, Kwamared Shehu Sani yayi kira ga ‘yan Najeriya da a koda yaushe su dinga hakuri tare da yiwa shugabannin su addu’o’i na fatan alkhairi.

Rahoton Dabo FM ya bayyana tsohon sanatan yayi ta kiraye kiraye ga al’umma cikin satin nan tun bayan da abubuwa suka ta’azzara a Najeriya.

Sakon da ya fitar a ranar Asabar ta shafinsa na sada zumunta ya bayyana “Ayi wa Baba uzuri, gyara sai a hankali, kauda talauci sai Allah, babu kyau aibata shugabanni.”

Ya kuma kara da cewa “A kowanne lokaci ku zama masu hakuri da yawaita addu’a ga shugabannin ku, babu mai azurtawa sai Allah, duk abinda kuka ga ya same ku dama yana rubuce a rayuwar ku. Idan shinkafa ta gagare ku kuci dabino.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog