Kano: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 4 gami da share gidaje 5,200 a Dambatta da Rogo

Karatun minti 1

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano, SEMA ta tabbatar da mutuwar mutum 4 gami da lalata gidaje 5,200 da ambaliyar ruwa ta yi a kananan hukumomin Rogo da Dambatta dake jihar Kano.

Rahoton Dabo FM ya bayyana sakataren hukumar, Sale Jili ya bayyana wa hukumar yada labarai ta kasa a ranar Asabar.

Tini dama wata hukuma tayi hasashen za a samu ambaliyar ruwan a kananan hukumomi 20 a fadin jihar Kano.

Malam Sale ya bayyana mana mutum biyu sun rasu ne a karamar hukumar Rogo tare da shafewar gidaje 200, kana a karamar hukumar Dambatta ma an samu rashin mutum 2 da lalacewar gidaje dubu 5.

Sakataren hukumar ya kuma bayyana mana cewa hukumar ta raba kayayyakin tallafi na kimanin miliyan 3 da rabi, wanda suka hada da Siminti, Kayan abinci, kwanukan rufi, katifu da dai sauransu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog