(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Nuna alhinin kisan wani dan Legas da shugaba Buhari yayi ya janyo cece-kuce

Karatun minti 1
Shugaba Muhammadu Buhari

‘Yan Najeriya sun nuna rashin jin dadinsu bisa nuna alhini da shugaba Muhammadu Buhari ya nuna kan kisan wani mutumin Legas da akayi, hakan ya biyowa ne bayan kashe-kashen da akeyi a garuruwan Zamfara, inda aka ji har yau shugaban baice wani abu game da kashe kashe da sace sacen ba.

Jim kadan bayan mutuwar mutumin da aka kashe dan jihar Legas, shugaba Buhari ya bayyana rashin jin dadinshi game da kisan, tare da aike sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan mamacin.

Fadar shugaban kasar ta fitar da ta’aziyyar tare da bada tabbacin hukunta wadanda suke da laifi wajen yin kisan a shafin ta na manhajar Twitter.

Sakon na zuwa ne daidai lokacin da ake samu rahotanni kisan gillar mutane sama da guda 50 a wannan makon daga jihar Zamfara.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa jami’an tsaro basa zuwa domin su basu kariya daga ‘yan bindigar dake aikata kisan gillar.

 

A makon da muke ciki ne aka samu rahotan bindigar wasu manoma guda 42 a kauyukan Kurya da makotansu dake karamar hukumar Shinkafin jihar Zamfara.

Saidai fadar shugaba Buhari bara ce komai akan wannan batun ba, duk da cewa hukumomin tsaro sun tabbatar da faruwar al’amarin.

Al’umma da dama dai nata tafka muhawara a shafin twitter, inda wasu ke cewa, “Gwamnati bata kulawa da kowa sai yarabawa.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog