Dan majalisa ya ɗauki nauyin yi wa direbobi katin shaidar tuƙi wato “Driver’s Licence”

Karatun minti 1

Bakwankwashen ɗan majalisar jiha, Lawan Sani Inuwa Guru mai wakiltar Guru Central dake jihar Yobe ƙarƙashin jam’iyyar PDP zai dauki nauyin yiwa direbobin motocin haya wanda suke ƙarƙashin karamar hukumar da yake wakilci katin shaidar tuki domin kawo ƙarshen hantarar da hukumomi suke musu.

Sanarwar da aka aikewa Dabo FM ta bayyana Mr LAS ya ce “A wannan karon mun waiwayi yan uwammu wasu direbobi wadanda basu da katin “Driver’s License” domin yi musu rigista tare da mallaka musu katin domin kaucewa hantara, da tsangama da biyan tara da suke fuskanta wurin jami’an tsaro a wasu lokutan.”

“Muna samun bayanai marasa dadi dangane da abinda ke faruwa da direbobin mu akan hanya sakamakon rashi wannan katin na “Driver’s License” wannan shi ne dalilin da yasa muka kudiri aniyar share musu hawaye.”

Ya kara da cewa “DUK MAI DRIVING SCHOOL CERTIFICATE AMMA COMMERCIAL ya Kira wannan number 08038326681–Tallafawa masu karamin karfi shi ne babban abinda muka sa a gaba domin ganin masu kananan sana’oi sun dogara da kansu.”

 

“Daga karshe, zamu ci gaba da bada gudunmawar cikin abinda Allah ya hure mana ga daukacin masu kananan sana’oi a garin mu domin karfafa musu” Jama’ah dan munyi abu mun baiyana ba laifi ba ne dan siyasa mu keyi-su lokacin da sukayi ra’ayin su ai sun baiyana NAGODE.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog