Yadda masu garkuwa da mutane suka tafi da Mai gidana-Khadija Sulaiman

dakikun karantawa

A daren Asabar din da ta gabata ne, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka shiga rukunin gidajen ma’aikata na makarantar kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya ta Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutane uku yayin da suke harbi daya a hannu.

Uwar gidan wanda aka yi awon gaba da shi mai suna Khadija Sulaiman, ta ce mai gidan nata mai suna Bello Atiku, ya dawo gida misalin karfe tara na dare sai ya tsaya a waje ya jima yana waya da wani mai gidan sa kan wani taro da za’a gudanar. Daga bisani ya shigo cikin daki kuma suka yi kallo tare da yara har suka kwanta.
Suna zaune ne sai suka ji ana buga kofar dakin, bayan sun fito ne sai suka yi kicibis da mutane biyu dauke da bindigogi suka naimi su kwanta a tsakar dakin, Bayan sun kwanta sai suka bukaci su basu wayoyin su Kuma suka tafi da wayoyin tare da mai gidan nata wato Injiniya Bello Atiku.

Ta kara da cewa rukunin gidajen nasu yana falalar fili ne ba tare da an killace su ba, shiyasa ma suka sami daman shigowa ba tare da wani fargaba ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban makarantar Injiniya Dakta Kabir Abdullahi ya ce barayin sun isa kwalejin ne da misalin karfe 9 na daren Asabar kuma suka yi awon gaba da ma’aikacin nashi, Kuma suna iya bakin kokarin su domin an bankado barayin tare da dawo da shi cikin iyalan sa cikin koshin lafiya.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa daya daga cikin ma’aikatan, Sunusi Hassan an harbe shi a hannu wanda ya tsallake rijiya da baya daga ‘yan ta’addan suka yi yunkurin sace shi kuma an garzaya da shi asibiti don kula da lafiyarsa.

Ya danganta lamarin da rashin kyawun makarantar wanda hakan ya sanya daliban kwalejin ga hatsarin da ba a zata ba.

Shi ma kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna Shehu Usman Makarfi ya ce suna iya bakin kokarin su domin kara yawan jami’an tsaron da ke aiki a makarantar, Kuma za su cigaba da duba yiwuwan daukar matakan da suka dace domin killace makarantar.
Kuma ya naimi ma’aikata da daliban makarantar su kwantar da hankulan su yayin da za’a cigaba da gudanar da harkokin karatu kamar yadda aka saba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog