Liverpool ta sha da ƙyar a hannun Leeds United ta ci 4-3

Karatun minti 1
Dan Wasa Muhammad Salah

Kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool ta sha da kyar a hannun Kungiyar Leeds United. An dai tashi daga wasan Liverpool na da 4, Leeds United na da 3.

Wannan wasan shi ne wasan farko da kungiyoyin suka buga a kakar wasanni ta 2020-21 da aka fara ta yau Asabar, 12 ga watan Satumbar 2020.

Kazalika wasan Firimiya League na farko da Kungiyar Leeds United ta buga bayan shekara 16 da ta shafe bata buga gasar Firimiyar ba.

Dan wasa Muhammad Salah ne ya jefa wa Liverpool kwallaye 3 inda Virgil Van Dijk ya zura kwallo daya. A bangaren Leeds United, ‘yan wasa J. Harrison, P. Bamford da M. Klich ne suka jefa wa Leeds United kwallaye a ragar Liverpool.

Zuwa yanzu, Arsenal ce a kan teburi da kwallaye 3 da maki 3.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog