Idan Masara ta gagareku, ku lashi zuma da Bisimillah – Shehu Sani ya sake rarrashin ‘yan Najeriya

Karatun minti 1
Kwamared Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna, Kwamared Shehu Sani ya yi kira ga ‘yan Najeriya da a koda yaushe su dinga hakuri tare da yi wa shugabannin su addu’o’i na fatan alkhairi.

Rahoton Dabo FM ya bayyana tsohon sanatan ya yi ta kiraye kiraye ga al’umma cikin satin nan tun bayan da abubuwa suka ta’azzara a Najeriya.

Wani sabon sakon da ya fitar a ranar Asabar ta shafinsa na sada zumunta ya bayyana “Idan Masara ta gagareka, ka lashi zuma, amma kafin ka lasa kayi Bismillah. In Shaa Allah za ka ji ka koshi.”
A satin da ya gabata ma, Tsohon sanatan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika cin dabino a duk lokacin da suka nemi Shinkafa suka rasa tare da yin kira da kara yin hakuri kan halin kunci da al’umma suka tsinci kansu a ciki tsamo-tsamo.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog