Kungiyar Barcelona ta kasar Spain ta sha kashi a hannun kungiyar Bayern munich ta kasar Jamus da ci 8 da 2 .
Wasan ya kasance na daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da ake karasa bugawa a kasar Portugal sakamakon tsaikon da cutae Koronabairas ta kawo.
Dan wasan kungiyar Bayern, Thomas Muller ne ya fara saka kwallo a ragar Barcelona a minti na 4 da take wasa.
Dan wasan kungiyar Bayern, Thomas Muller ne ya fara saka kwallo a ragar Barcelona a minti na 4 da take wasa.
David Alaba na bayan Munich ya ci gida a minti na 7 kafin daga bisani dan wasa Perisic na Bayern ya jefa kwallo a ragar Barcelona a minti na 22.
Ga yadda ta kaya cikin hoto;

Bayern Munich za ta kara da Manchester City ko Lyon a wasan daf da na karshe a gasar ta bana.
