Ra’ayoyi: Buhari a dafa su, Ganduje a soya su – Matashi

Tin bayan fitowar wasu faifayen bidiyoyi a waje da yayi kama da kasuwar Waya ta Farm Center dake jihar Kano, bidiyon na wani mutun mai sana’ar siyar da takalma cikin waken kiran kasuwa.

Bayan nazari da ‘dan bincike da muka gudanar, mun gano cewa mutumin yana wakar ne bisa yanayin tsanani da mutanen jihar Kano dama Najeriya gaba daya.

Wakilin mu a nan Dabo FM, ya gano mana wasu daga cikin irin maganganun da mutumin yake yi a cikin waken.

Ya fara da yiwa shugaba Muhammadu Buhari addu’ar karin lafiya, kafin daga bisani ya fara jero baituka kamar haka;

"Allah ya kara ma lafiya Baba, kaji dadin ragar-gazar mu."
Buhari a dafa su, Ganduje a soya su. (x2)

Afi ragar-gazar bangaren Arewa, sunfi rashin ji.
Buhari a dafa su, Ganduje a soya su. (x2)

A arewar ma afi ragargaza Hausawa, sunfi isk***.

Ganduje a soya su.
Su suka zabi a soya su (x8).

Sako na musamman

Masu Alaƙa  Shugaba Buhari ya dauki hanyar zuwa kasar Jordan da Dubai

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: