Labarai

Kano: CP Wakili ya kama katan din Tramadol 303

Yau Juma’a Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kwace katan din Tramadol 303.

Da yake yiwa manema labarai jawabi, Kwamishan yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili yace sun samu nasarar kwace magani ne bayan hada jami’ai na musamman domin gudanar da aikin.

Majiyoyin Dabo FM sun bayyana mana cewa; CP Wakili yace an kama maganin ne a waje mai lamba 157 akan Titin Miller dake unguwar Bompai a karamar hukumar Nassarawa.

Lokacin sumamen, jami’an ya sandan sun afka cikin wani dan karamin kamfanin hada magunguna mai suna ‘Ugolab Manufacturing Company’ wanda yake da zama a unguwar ta Bompai.

Wakili yace sun kama Chris Metuh da suke zargi kuma ya bayyana cewa yanzu haka yana hannun jami’an ‘yan sandan.

Ya kara da cewa “Kunga yacce ake harkar miyagun kwayoyi a Kano.”

Ya ce yayi mamaki yacce ake iya ajiye maganin mai matukar yawa a gida haka kuma har ake samu a rabar dashi zuwa guraren da suke kaiwa.

Punch ta rawaito Wakili yana cew; “Zan cigaba da neman goyon bayan mutane dan hukumar ‘ya sanda ta samu nasarar kakkabe jihar Kano daga dukkanin laifuka da hrkar miyagun kwayoyi.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Hotuna: Ziyarar CP Wakili ga wasu daga cikin manyan Malaman jihar Kano

Dabo Online

Kano: Dole a fadi sakamakon zabe kafin sallar Isha – Kwamishina Wakili

KANO: CP Wakili ya dawo bakin aiki bayan tafiyar DIG Ogbizi

Dabo Online

Kano: CP Wakili ya kama ‘Yan fashi da masu dillancin Kwayoyi 142 a kwana 4

Dabo Online

ZabenKano: ‘Yan sanda sun cafke mataimakin Ganduje, bayan yunkurin sace takardar tattara sakamako

Dabo Online

Amana: Wa’adin aikin CP Wakili ‘Singham’ yazo karshe

Dabo Online
UA-131299779-2