(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu

dakikun karantawa
Sarkin Zazzau
Mai martaba Alhaji Shehu Idris -Sarkin Zazzau

Mai martaba Sarkin ZazZau, Alhaji Dr Shehu Idris ya rasu yau Lahadi, DABO FM ta tabbatar.

Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin ya rasu ne yau Lahadi a birnin Abuja  bayan fama da gajeriyar  rashin lafiya.

Sarkin Zazzau
Mai martaba Alhaji Shehu Idris -Sarkin Zazzau

An haifi mai martaba Sarki a shekarar 1936, ya bar duniya yana da shekara 84.

Ya zama Sarkin Zazzau a shekarar 1975.

Ga tarihin Marigayi da Sashin Hausa na BBC ya tatattara.

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi ne Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi da ne, dan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo.

Shi kuma Sarki Muhamadu Sambo da ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim. Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a daular Fulani karkashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Danfodiyo ya yi a kasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a sarautar Zazzau.

Shi Mai martaba Sarki lokacin mahaifinsu yana Mai Unguwa a unguwar Iya a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata unguwa ce da ke tsakanin unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara akalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini.

A nan dai unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya, wadda ake kira ‘Town School one’, ita ce kuma makaranatar ‘Kofar Kuyanbana Local Government Education Primary School’. Yanzu ana ce mata ‘Waziri rLawal Local Government Education Primary School’, a nan ya fara karatu.

Bayan ya gama sai ya tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan ‘Middle School’. Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina lokacin ana kiran ta ‘Katsina Teachers’ College’.To, a nan ya koyi aikin koyarwa, wanda shi ne babbar sana’arsa ta farko da ya iya.

Daga baya mai martaba ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar Ostireliya (Australia). Yana cikin daliban farko da ofishin jakadancin Ostireliya suka dauki dawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki a kasar ta Osireliya.

Wuraren da ya yi aiki

Daga shekarar 1956 ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da kauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar ‘Town School No.3”.

A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da ya koma karkashin hukumar ‘NA’ (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu. Inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar ‘NA’, kuma yana aiki a matsayin jami’in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa.

Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin ‘Native Authority’ a wannan lokacin. – BBC Hausa

Karin Labarai

Sabbi daga Blog