Copyrighted.com Registered & Protected

Zaben2019: Ba’a kama wani matashi ‘dan PDP da bugaggen sakamakon zabe ba, labarin bogi ne – Hukumar ‘Yan sanda

Hukumar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom tace rahotan da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta, ba wani abu bane illa bogi.

Rundunar tace batada da wata masani game da cafke matashin da ake zargi da yawa da kayan magudin zabe, ciki harda bugaggen sakamakon zabe na bogi.

Kakakin rundunar shiyyar jihar Akwa Ibom, SP Geoffrey Ogbonna ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar batada wata masani.

“Nima na karanta wannan labari a wata kafar sada zumunta, amma daga bangarenmu, a hukumance bamu da wannan labarin.”

Manema labarai sun nemi jin ta baki hukumar ‘yan sandanne bayan da mai magana da yawun jami’iyyar APC na jihar Akwa Ibom, Mr Godson Benedict yace suna kama matashin da ake zargi, kuma sun mika shi zuwa jami’an tsaro domim yin bincike.

Kafafen sada zumunta a jiya sunyi ta wallafa labarin wannan matashi da ake zargi da ‘da ne na jami’iyyar PDP, kuma majiyoyin sunce an cafke shi da bugaggen sakamakon zabe da yake nuni da nasara jami’iyyar ta PDP.

Hukumar zabe ta INEC ta dage zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar dattijai da wakilai har zuwa 23 ga watan Fabarairu.

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na facebook.

%d bloggers like this: