/

Boko Haram ta hallaka mutum 17 a Borno

Karatun minti 1

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane 15 tare da yin awon gaba da mutun 12 a wasu hare-hare data kai a karamar hukumar Jere da Gwoza dake jihar Borno.

‘Yan bindigar da ake zarga da mayakan Boko Haram sun kai harin ne a safiyar jiya a cikin garin Maiduguri.

Wani mai shedar gani da ido ba bayyanawa manema labarai cewa, a lokacin da maharban suna harbi, wasu daga cikinsu suka fara bi gidajen mutane suna daddasa abubuwan fashewa, lamarin da kai ga mutuwar kansu da karin mutum 11 daga mutanen gari. -Kamar yadda jaridar Daily Trust rawaito.

Rundunar yan sandan jihar Borno ta tabbatar da faruwar al’amarin a wata sanarwa da Kwamishinan yan sandar jihar ya bayyana, yace mutane 11 ne suka rasa rayukansu, 15 suna karbar magani.

“Mutane sha biyar da aka harba, a yanzu haka suna asibiti domin karbar agajin gaggawa.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog