OGUN: Jami’in Kwastam ya kashe mutum, akan cin hancin N5000

Karatun minti 1

A wani faifan bidiyo da Victor Bola Alade, ma’aikaciya wani gidan talabijin ta wallafa a shafinta na facebook, yayi nuni da wani jami’in kwastam ya harbe wani bawan Allah har lahira akan rashin bada cin hancin naira dubu biyar.

An jiyo mai daukan bidiyon tana kuka yayin daukar bidiyon kuma tana cewa “You killed him because of N5000 oo”

“Kun kashe mutum saboda naira dubu biyar.”

 

Matasan wajen sun fusata ta hanyar yi wa jami’an kwastam din dukan kawo wuka, kuma suka hanasu tafiya daga wajen faruwar al’amarin, tini dai aka garzaya da jami’an asibiti domin karbar agajin gaggawa.

 

Al’amarin ya faru ne yau Lahadi 17 ga watan Fabarairun 2019, a kan titin Shagama dake garin Shagamu da misalin karfe 2:40 na rana.

Sai dai a nata bangaren, hukumar ta Kwastam tace, jami’in yayi harbin ne bisa zargin matashin da safarar kayan gwanjo, kayan da hukumar ta hana shigowa dasu kasar Najeriya.

Da aka zantawa da wani shedar gani da ido, bayyana jami’an sun kashe mutumine akan rashin bada N5000 da jami’an suka bukata.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog