(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Borno: Zulum zai gudanar da zaben kananan hukumomi bayan shekaru 15 na rashin gudanar da zabukan

Karatun minti 1

Za a gudanar da zaben kananan hukumomi ajihar Borno, kasancewar sama da shekaru 15 da rashin gudanar da zaben.

Wakilin Dabo FM a garin Maiduguri, Ibrahim Mustapha ya rawaito mana gwamna Babagana Umara Zulum yace “Hakika jihar Borno jahace kamar ko wace jaha a tarayyar Najeriya dan haka yazama dole a gudanar da zabukan kananan hukumomi afadin jihar.”

Ya kara da cewa “Hakan yazo ne duba da yadda aka dibi shekaru batare da angudanar da zabukan kananan hukumomin guda 27 ba.”

Zulum ya bayyana cewa “Hakika rashin gudanar da zaben tamkar wani yunkuri ne na musgunawa kananan hukumomin duba da yadda suke da karantattu a cikin su, dan haka amatsayi na na shugaba bazan amince da tafiya a haka ba dole ai zabe a duk fadin jaha dan gudanar da komai cikin nutsuwa.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog