Shahidai goma sha biyu masu daraja – Daga Sheikh Hamza Uba Kabawa

dakikun karantawa

Taskar Malamai daga Dabo FM tare da Sheikh Hamza Uba Kabawa, babban limamin masallacin juma’a na kasuwar Singa a jihar Kano.

Tarihin Musulunci cike yake da gwaraza da suka bayar da jininsu saboda Allah. Da jininsu ne bidhiyar Musulunci ta fito , ta yi yaɗo, ta kafu kuma ta yaɗa rassa a duniya.

Daga cikin irin waɗannan shahidai akwai guda goma sha biyu masu ƙololuwar daraja kamar haka :-

1- Sumayya Bint Khayyaɗ , mahaifiyar Ammar Bn Yasir. Ana yi mata alkunya da Ummu Ammar. Ta yi shahada a Makka kafin Hijira da shekara bakwai.
2- Ubaidullahi Bn Al Harith Bn Abdulmuɗɗalibi. Ana yi masa alkunya da Abul Harith. Ya yi shahada a yaƙin Badar shekara ta biyu bayan Hijira. Ɗan uwa kuma ƙani ga Manzon Allah saw. Yana daga cikin mutum ukun farko da suka yi mubaraza da kafirai a Badar.
3- Mus’ab Bn Umair, ana yi masa alkunya da Abu Abdullahi. Ya yi shahada a yaƙin Uhud shekara ta uku da Hijira.
4- Hamza Bn Abdulmuɗɗalib, shugaban shahidai. Ana yi masa alkunya da Abu Ammarata. Ya yi shahda a yaƙun Uhud shekara ta uku da Hijira.
5- Ja’afar Bn Abi Ɗalib, ɗan uwan sayyadina Ali. Ana yi masa alkunya da Abu Abdullah. Ya yi shahada a yaƙin Mu’atata shekara ta takwas da Hijira.
6- Umar Bnl Khaɗɗab, Amirul mu’aminin. Ana yi masa alkunya da Abu Hafsin. Ya yi shahada a masallacin Manzon Allah a shekara ta ashirin da uku da Hijira.
7- Usman Bn Affan, Abu Abdullah. Amirul mu’aminin. Ya yi shahada a gidansa a Madina shekara ta talatin da biyar da Hijira.
8- Zubair Bn Awwam, Abu Abdullahi. Ya yi shahada lokacin yakin Jamal a shekara ta talatin da shida da Hijira.
9- Ɗalhatu bn Ubaidullah, Abu Muhammad. Ya yi shahada a yaƙin Jamal shekara ta tslatin da shida da Hijira.
10- Ammar Bn Yasir, Abul Yaƙzhan. Ya yi shahada a yaƙin Siffin shekara ta talatin da bakwai da Hijira.
11- Aliyu Bn Abi Ɗalib, Abul Hasan. Amirul mu’minin. Ya yi shahada a Kufa shekara ta arbain da Hijira.
12- Husain Bn Ali Bn Abi Ɗalib, Abu Abdullah. Ya yi shahada a Karbala shekara ta sittin da ɗaya da Hijira.
Biyar daga cikin waɗannan suna cikin waɗanda akaiwa bushara da Aljanna guda goma a hadisi ɗaya.
Shida daga ciki kafirai ne suka kashe su. Shida kuma musulmi ne suka kashe su.

Uku daga daga ciki sun yi shahada akan gadon halifanci kuma dukkaninsu sirikan manzon Allah ne.
Shida daga ciki ƴan uwan manzon Allah ne na jini ( Ahlul Baiti ).
Allah ya karɓi shahadarsu, Ya girmama ladansu , Ya ɗaukaka darajarsu.

Musulunci bai yi umarni da zaman makokin wani daga cikinsu ba ko juyayin tunawa da shahadarsu.
Abin da zamu ce ga mabata shi ne ” Allah ka fafarta mana da ƴan uwanmu da suka rigaye mu a imani. Kada ka sanya gaba da kiyayyar wani mumini a cikin zukatanmu.Haƙiƙa ya Ubangiji kai mai rahama da jin ƙai ne “

Karin Labarai

Sabbi daga Blog