Yadda babbar hanyar Buji a jihar Jigawa ta shafe, mutane sun koma hawan Amalanke

dakikun karantawa

Saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya ya shafe babbar hanya shiga garin Gantsa a dake karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.

Wakilin DABO FM ya ganewa idanuwansa yadda mamakon ruwan ya rufe hanyar shiga karamar hukumar musamman hanyar da ta nufi babbar hedikwatar karamar hukumar ta Buji.

Kamar yadda zaku gani cikin hotuna, mutane da ke son shiga ko fitowa daga garin su kan bi ta cikin ruwan da ya kusa kai wa gwiwowinsu, inda masu babura suke sauka daga kan babur su tura.

Yayin da wasu suka yanke shawarar komawa hawan amalanke domin saukaka zirga-zirga a yanki.

DABO FM ta tattara cewar kusan kowacce damuna, a kan samu rufewar hanyar, lamarin da har yanzu an kasa shawo kanshi domin saukakawa al’umma.

A bara dai ruwan ya shiga garin ne ta yankin kudu da garin, wato in ka bar garin Kawaya, amma a bana, kuma Ruwan ya rufe hanyar Arewa da garin ne, wato kafin kai wa ga  Titin Maiduguri.

Bisa ga alamu da kuma yadda damunar take kara karfi, ruwan zai iya mamaye gabar har ya kai ga babu wanda zai iya wucewa ta wajen.

Wasu da suka zanta da DABO FM sun yi kira ga gwamnati da kwamishinan ayyuka a jihar Jigawa da su taimaka su duba hanyar domin kai musu dauki.

“Muna kira ga mai girma Gwamna da kwamashinan Ayyuka da su taimaki al’ummar wannan karamar Hukuma, domin wannan hanya ita ce gatan karamar Hukumar baki daya.

Kamar yadda aka sanar an bada aikin hanyar, don Allah a sanarwar dan gwangilar hanyar ya zo ya fara aiki, domin jama’a suna cikin wani yanayi.” – cewar mutanen.

6524-B9-D5-2-B74-40-FB-A8-B2-D8-F34-A4-AD50-F
DC6-F58-B2-56-D8-47-FA-A593-727-BC9838-B4-B
6-FB52-FB5-C757-4-A0-C-81-F1-815494-CB1-E22
B718-DAFE-F606-4-B5-C-ABA6-34-EA79750-F71
029-A273-D-E559-4-C01-ABF9-0-DF33722516-C

A wani labarin kuma, DABO FM ta bude sashin Taskar Dabo, sashi da zai riko fito da Jaridar yanar gizo-gizo ‘E-Newspaper’ ta nau’in PDF daga Lahadi, satin farkon watan Satumba 2020.

Sabon babban editan Jaridar, Mu’azu Abubakar Ahmad Albarkawa ne ya sanar da haka a yayin jawabinsa na karbar mukamin edita.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog