Gidauniyar Kwankwasiyya ta kai karin dalibai kasar Dubai da Sudan domin karatun digiri na 2

Gidauniyar Kwankwasiyya ta jihar kano ta dau nauyin dalibai tara don tafiya kasar Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa domin yin digirinsu na biyu.

Dabo FM ta tattara cewar bakwai daga cikin daliban zasu yi karatun a fannin ilimin addinin Musulunci ne da harshen larabci a kasar Sudan inda sauran biyun zasu karanci fannin kasuwanci ne a Dubai.

A yayin jawabi ga daliban jim kadan kafin tashinsu, tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa sune kaso na karshe na dalibai 370 da gidauniyarsa ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasar Indiya da wasu kasashen duniyar nan.

Kwankwaso ya ce yau ta kasance rana mai dumbin tarihi don ya cika alkawarin da ya dauka na daukar nauyin ci gaban karatun matasa a ciki da wajen Najeriya. “Wannan rana ce mai dumbin tarihi wacce muka cika alkawarinmu na ci gaba da daukar nauyin mata da matasa don ci gaba da karatunsu,” ya jaddada.

Masu Alaƙa  #NigeriaDecides2019: Atiku ya lashe akwatin gidan Kwankwaso

Sanata Kwankwaso, wanda ya wakilci jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai ta 8 ya yi kira ga daliban da su dau karatunsu da matukar muhimmanci tare da kasancewa jakadai na gari ga jiharsu da kasarse a yayin da suka sauka a Sudan da Dubai.

Kamar yadda ya ce, gidauniyar ta biya musu kudin makaranta, wajen kwana, abinci da kuma kudin kashewa. Haka kuma ya bukaci daliban da su kasance jakadun Kwankwasiyya nagari, jihar Kano da kuma Najeriya.

Ya ce duk wanda yayi kuskure ba zai tafi haka ba, watau ba tare da an hukunta shi ba. Ya ce gidauniyar za ta ci gaba da bin kwakwafin karatun nasu a makarantun da suka tafi.

Masu Alaƙa  Yanzu an mayar da sarakuna a Kano basu da wata daraja -Aminu Daurawa

Babban malami a jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ja kunnen daliban a kan nuna wata dabi’a da kan iya bata sunan jihar Kano da Najeriya a kasar da suke je da kuma idon duniya.

A watan Satumbar da Oktobar 2019, daliban gidauniyar sama da 240 suka sauka a kasar Indiya domin yin karatu a wasu daga cikin manyan jami’o’in kasar da suka hada da Sharda Univeristy.

Haka zalika DABO FM ta samu ziyartar daliban a lokacin da tsohon Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai wa daliban ziyara a birnin Greater Noida dake jihar Uttar Pradesh kusa da babban birnin New Delhi a ranar 5 ga Nuwamba a 2019

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.