Yakamata Mata su rungumi sana’o’in dogaro da kai – Habeeba S Lemu

Zaurenmu na Taskar Matasa na yau ya zanga da wata matashi yar asalin jihar Nijar a Najeriya da take sana’ar kwalliyar zamani ga ‘ya’ya mata.

Habeeba S Lemu, matashiya dake sana’ar kwalliyar zamani ta mata, tayi kira ga mata su rungumi sana’o’in domin samun rufin asiri da zai saka su dogara da kansu.

Yayin wata ganawar matashiyar da jaridar Leadership, Habeeba S Lemu ta bayyana riko da sana’a a matsayin wata kariya ga mata wacce zata kare su daga wulakanci ko roko a wajen mazaje da suke amfani da wannan damar wajen yin lalata dasu.

Yayin zantawar DABO FM da matashiyar ta bayyana fara sana’arta tin shekaru kusan 6 da suka gabata, sana’ar da ta sanya wa suna da ‘Glamours’, tare da yadda ta iya hada karatun da takeyi na aikin jarida da kuma gudanar da sana’ar ba tare da samun cikas ba.

Masu Alaƙa  Ko Sarkin Kano da Ganduje sun shirya ya kamata a kammala bincike - Barr Abba Hikima

“Na fara koyan kwalliya ne tun ina karama, tun kafin insan zai zata zamemin sana’ar hannu na, saboda ina sha’awar yin kwalliya sosai, na kan zauna a gaban madubi na tsawon lokaci yayin kwalliya, har na kware daga nan ne na yi shawarar mayar dashi sana’ata, tun ina yi wa mutanen gida har na fara yi wa makwabta daga nan wasu suka fara zuwa daga nesa, har kuma nayi shawarar fara sana’ar gaba daya.”

Ta kuma bayyana irin nasarorin da ta samu a tsawon lokacin da ta dauka tana gudanar da sana’ar. Kama daga samun kudi da yi wa iyayenta sha tara ta arziki da kuma samun yabon wadanda take yi wa kwalliyar.

Masu Alaƙa  Zuwa ga masu neman a baiwa Mata limancin Sallah da nufin 'Kare hakkin Mata' daga Bin Ladan Mailittafi

Daga karshe tayi kira ga jami’in mata da suka hada da matan aure, zaurawa da yan mata da su rungumi sana’a domin dogaro da kawunansu.“Shawara ta ga matasa yan uwana shi ne su tashi tsaye su koyi sana’ar hannu koman kankantarsa kada su raina sana’a, matukar za ta rufa musu asiri, ta haka za su samu cikakken mutunci a tsakanin abokansu, za kuma su samu na tallafa wa iyayensu da ‘yan uwansu.“

Ga masu son ayi musu kwalliya zasu iya tuntubarta a shafinta na Instagram @glamourous_s.l

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.