//
Thursday, April 2

El Rufa’i ya kara mafi karancin albashin yan fansho daga N3000 zuwa N30,000

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya mayar da N30,000 a matsayin albashi mafi karanci na yan fanshon jihar Kaduna.

Babban mataimakin gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan da reshen Kungiyar yan Fansho ta Najeriya reshen jihar Kaduna ta yabawa gwamnan bisa karin da yayi daga N3,000 zuwa N30,000 a kowanne wata.

Yace Kungiyar ta yaba wa gwamnan bisa kula da kula da al’amarin tsofaffin ma’aikatan jihar bisa ga karin albashi tare share musu hawayensu.

Ya kara da cewa karin na zuwa ne bayan da wasu yan fansho suka kai wa gwamnan kukansu yayin da yake gabatar da wata hira a gidan rediyon jihar, inda suka bayyana masa cewar suna karbar N3000 zuwa N7000 a kowanne wata.

Masu Alaƙa  Yanzu-Yanzu: El-Rufa'i ya bawa Sanusi II Murabus babban mukami, kwana 1 da sauke shi

Haka zalika sanarwar tace lallai gwamnan ya tabu bisa ga irin halin da ya ‘yan fansho suke ciki wanda hakan yaga dacewar a canza tsarin albashin nasu.

Da wannan karin, sanarwar tace kudaden fanshon jihar zai karu da Naira miliyan 200, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya rawaito.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020